
Masu sanya idon dai sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Accra babban birnin ƙasar ta Ghana.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Muhammad Namadi Sambo da ya jagoranci tawagar ECOWAS wajen sanya ido a zaɓen, ya ce an baiwa al’ummar ƙasar dama wajen zaɓen wanda suke so ya jagorance su.
Sama da al’ummar Ghana miliyan 18 ne suka kaɗa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da kuma na ƴan majalisu 276 da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Ku latsa alamar sauti don sauraron rahoton wakilinmu Sham-un Bako........
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI