Masu kaɗa ƙuri'a a Ghana sun fito domin zaɓar wanda zai shugabancesu a ƙasa

Masu kaɗa ƙuri'a a Ghana sun fito domin zaɓar wanda zai shugabancesu a ƙasa

A yau 7 ga Disamba, 2024 ake sa ran Ghana za ta zabi sabon Shugaban Kasa inda kasar ke sauraron cika alkawururrukan manyan 'yan takara kan farfado da tattalin arziki a lokacin da kasar tra Yammacin Afirka ke fuskantar tsadar rayuwa da hauhawar farashi.

Manyan 'yan takarar shugaban kasa a zaben Gana John Dramani Mahama da Mahamudu Bawumia sanannu ne a fagen siyasar Gana.

'Yan takara goma sha biyu, masu jefa kuri'a da suka fahimci siyasa, da kuma kasar da ke sa ran samun abubuwa da dama.

A yayin da Gana ta shirya gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 7 ga Disamba, ana gaf da kammala yakin neman zabe inda ake ganin yadda manyan 'yan takara za su fafata.

Wanda zai gaji shugaba Nana Akufo-Addo da ke kammala wa'adinsa na biyu a ofis, zai fito ne daga cikin wadannan 'yan takara biyu na jam'iyyar NPP mai mulki da na jam'iyyar adawa ta NDC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)