
Hukumomin sun ce Maharan sun ƙaddamar da aika-aikar ce a ranar juma’ar da ta gabata a tsakanin biranen arewacin Gao da Ansongo.
A yayin da wani daga cikin tawagar da ya samu kuɓuta da ƙyar ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun musu kwanton ɓauna ne a yayin da suka buɗe musu wuta irin na kan mai uwa da wabi suna cikin tafiya, a ƙoƙarinsu na kashe mutane da dama.
Sojojin Mali da na Wagner na cikin wasu motoci ne kusan guda 10 domin baiwa ayarin ƙananan motoci ƙirar bas guda 22 dake ɗauke da fararen hula kariya, da wasu manyan bas-bas guda shida sannan da manyan motoci takwas, a yayin da aika-aikar ta faru.
Sannan wata kafar ayyukan kiwon lafiya ta ƙasar ta bayyana cwa ankai mafi akasarin waɗanda suka mutu tare da wasu da suka jikkata birnin Gao wani babban birni dake arewacin Mali.
Sai dai a yayin harin, ‘yan ta’addar sun tarwatsa manyan motocin dakon kaya 5, sannan ƙungiyar IS ta masu ikrarin jihadi bata ce komai dangane da mummunan harin ba.
Ƙasar dake Afirka ta yamma ta samu kanta a cikin ruɗani ne ta hanyar fukantar juyin mulki babu ƙaƙƙautawa tun daga shekarar 2012, sannan kuma take fuskantar matsalar rashin tsaro musamman a rewacin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI