Shekara guda da ta gabata, birnin Timbuktu da kansa ya fuskanci babban shinge. Daga yanzu, samun damar zuwa Léré zai yi wahala domin a cewar wani mazaunin yankin da ke aiki a garin, hanyar da ta haɗa Léré zuwa Niono da kuma, zuwa Bamako, ta yanke gaba ɗaya.
Hakanan ga manyan motocin da ke zuwa daga Mauritania: "Dole ne mu yi jigilar kayayyaki a bakin kogin a kan tudu daga Mopti", wannan mai jigilar kayayyaki ya shaida, wanda ya kara da cewa ambaliya ta kara dagula lamarin.
Motoci daga Aljeria na iya, duk da haka, sun shiga Léré, a cewar wasu majiyoyi.
Babu karancin abinci a garin, amma shaidu sun ba da rahoton bacewar kayayyaki da yawa - madara, taliya, mai ,da kuma karin farashin.
Har ila yau, shingen da mayakan masu ikirarin jihadi na Jnim suka yi yana da nauyi a kan babban birnin.
Don isa kudancin kasar Mali, motoci a yanzu sun yi wani babban zagaye ta hanyar bin hanyar Douentza, sannan Mopti.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI