Rahotanni daga rundunar tsaron kasar na bayyana cewa harin ya faru ne yayin wani sintiri a ranar Litinin, sojojin kasar da dama ne suka samu rauni, a cewar wani babban jami'in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
A hukumance dai rundunar ba ta bayar da wata sanarwa kan wannan lamari ba.
Da jimawa hukumomin Benin suka daina bayar da bayanai game da abubuwan da ke faruwa a arewacin kasar inda sojoji ke fuskantar kungiyoyi masu dauke da makamai.
A watan Yuni, an kashe sojoji bakwai a wani hari da aka kai a wurin shakatawa na Pendjari.
A ranar 3 ga watan Disamba, an kashe sojoji uku a Malanville dake arewa maso gabashin kasar, kan iyaka da Nijar, daga hannun wasu mutane dauke da makamai.
Hare-haren da ake kai wa a arewacin Benin ya karu a shekarun baya-bayan nan kuma hukumomi na danganta su da mayaka masu ikirarin jihadi na kungiyar IS da kuma Al-Qaeda da suka fito daga kasashe makwabta inda suke da karfi.
Yankin kan iyaka da Burkina Faso ya kasance cibiyar hare-haren.
A watan Janairun 2022, Benin ta tura sojoji kusan 3,000 don kare iyakokinta a wani bangare na Operation "Mirador".
Hukumomin kasar Benin sun kuma dauki karin sojoji 5,000 domin karfafa tsaro a arewacin kasar. A karshen watan Afrilu, Tarayyar Turai ta sanar da cewa za ta saki Yuro miliyan 47, musamman ta hanyar siyan kayayyaki da kayan aiki, domin tallafa wa kasar Benin a yakin da take yi da ta'addanci. Kasashen Ghana da Togo da ke makwabtaka da Benin ma sun sha fama da hare-haren masu ikirarin jihadi a shekarun baya-bayan nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI