Shugaban ƙungiyar Chido Onumah ya bayyana haka a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da ke gudana a Najeriya, inda ya ƙara da cewar a ƙasashen Afirka ta Yamma kawai, Ghana ce ta samar da dokar da ke bai wa irin waɗanan mutane kariya.
Onumah ya ƙara da cewar babu irin wannan kariyar da ake buƙata a ƙasashe irin su Najeriya da Benin da Burkina Faso da Cape Verde da Gambia da kuma Guinea.
Sauran ƙasashen da ake buƙatar ganin sun ƙara ƙaimi wajen samar da dokokin sun hada da Guinea-Bissau da Senegal da Saliyo da kuma Togo.
Jami'in ya ce duk da yake ƙasashen sun rattaba hannu a ƙudirorin Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da yaƙi da cin hancin da rashawa, rashin samar da dokokin da ake buƙata na yiwa shirin illa.
Taron ya nuna damuwa da dokokin kare masu tsegunta cin hanci a Najeriya da aka samar a shekarar 2016 saboda rashin ƙarfinsa, duk da yadda ya bada damar gano maƙudan kuɗaɗen da jami'an gwamnati suka sace.
Taron ya ce yana buƙatar samar da dokar da za ta boye wanda ya gabatar da bayanan da aka gano irin waɗannan kuɗaɗe domin kare su da duk wata barazanar da ka iya tasowa daga waɗanda ake tuhuma ko kuma ƴan uwansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI