Masu fafutuka a Sudan sun ce dakarun RSF sun kashe aƙalla mutane 124 El Gezira

Masu fafutuka a Sudan sun ce dakarun RSF sun kashe aƙalla mutane 124 El Gezira

Tun bayan mika wuya da ɗaya daga cikin manyan kwamandojin RSF Abuagla Keikal ya yi ga sojojin ƙasar a ranar Lahadin da ta gabata, dakarun RSF ta kai hare-hare jihar da ya fito, tare da kashe fararen hula da kama wasu da dama tare kuma da raba dubbai da muhallansu.

Jihar Gezira na fuskantar rikici cikin watannin baya-bayan nan,  inda mazauna yankin suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, dakarun RSF na sace kayayyaki a gidaje da kashe fararen hula da dama tare da raba daruruwan mutane da gidajensu.

A cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu fafutukar ta fitar a yau ɗin nan, ta ce a kauyen Al-Sireha da ke arewacin jihar, dakarun RSF sun kashe aƙalla mutane 124 tare da raunata wasu ɗari.

Izuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ɓangaren rundunar sojojin Sudan da kuma dakarun RSF basu ce komai kan wannan batu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)