Masar za ta girke dakarunta a Somalia don yaƙar ƙungiyar al Shabaab

Masar za ta girke dakarunta a Somalia don yaƙar ƙungiyar al Shabaab

Wannan mataki na Masar na zuwa a dai dai lokacin da wa’adin dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika ke shirin kawo ƙarshe a ƙasar ta ƙuryar gabashin Afrika wadda ta shafe tsawon shekaru ta na fama da matsalolin tsaro.

Bayan wani taro da ya gudana a birnin Asmara fadar gwamnatin Eritrea cikin makon nan, shugaba Abdel Fatta Al sisi da kansa ya miƙa buƙatar girke dakarun na shi a Mogadishu bayan da ƙasashen na Masar da Somalia da kuma Eritrea suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro.

Cikin watan Disamban shekarar nan ne aikin dakarun na Afrika zai kawo karshe wanda zai bayar da damar ficewar dakarun ƙetare daga Somalia, sai dai al Sisi ya ce da zarar dakarun sun fice kai tsaye zai girke wasu don baiwa ƙasar kariya.

Tun bayan da Somalia ta samu ɓaraka da maƙwabciyarta Habasha ne, ƙasar ta karakata akalarta ga Masar wadda itama ke takun saka da Habashan.

Al Sisi wanda bai faɗi yawan dakarun Masar da zai girke a Somalia ba, bayanai na nuna cewa kai tsaye za su maye gurbin dakarun Afrika da ke cikin ƙasar tun shekarar 2007 don yaƙar al-Shabaab mai biyayya ga al-Qaeda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)