Ma’aikatar lafiya ta Masar ta ce an aike da motocin asibiti aƙalla 28 zuwa wajen da haɗarin ya faru a babbar hanyar Al-Galala wadda ta haɗa manyan yankunan na Masar biyu ciki har da Ain Sokhna.
Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Masar ciki har da jaridar Al-Ahram mallakin gwamnati sun bayyana cewa haɗarin ya rutsa da ɗaliban jami’ar Galala da ke birnin Galala.
A cewar rahotanni haɗarin ya faru ne lokacin da matuƙin motar ke sharara gudun da ya wuce ƙima kuma motar da kufce daga hannunsa.
Tuni dai mahukuntan Masar suka yi umarnin fara bincike don gano musabbabin haɗarin motar musamman bayan fitr jita-jitar da ke alaƙanta faruwarsa da gangancin matuƙin motar.
Masar na sahun ƙasashen arewacin Afrika mafi fuskantar haɗarin mota inda a 2021 kaɗai mutane dubu 7 da 101 suka rasa rayukansu sakamakon haɗarin, wanda ke nuna ƙarin kashi 15.2 idan an kwatanta da alƙaluman 2020.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI