Masar ta fara kwace kadarorin mambobin kungiyar 'Yan uwa Musulmi

Masar ta fara kwace kadarorin mambobin kungiyar 'Yan uwa Musulmi

Kotu a Masar ta yanke hukuncin kwace kadarorin mambobin kungiyar 'Yan uwa Musulmi su 89 tare da mayar da su mallakin gwamnati.

Labaran da jaridar Al-Akhbar Al-Yaum mai alaka da gwamnati ta fitar na cewa, kotun Alkahira ta yanke hukuncin karar da wata hukuma ta kai na neman a kwace dukiyoyin mambobin 'Yan uwa Musulmi.

Kotun ta yanke hukuncin a kwace kadarorin Shugabannin kungiyar su 89 da suka hada da Zababben Shugaban Masar na Farko Muhammad Mursi, matarsa da 'ya'yansa.

Kotun ta ce, wannan hukunci ya shafi magadan marigayi Shugaba Mursi da suka da matarsa Najla Ali Mahmud, da 'ya'yansa Shaima, Usama da Umar.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam da ke wajen Masar ta bayyana hukuncin da aka fake da sunan yak da ta'addanci, a matsayin yunkurin kwace dukiya 'yan kasa ta hanyar zalunci.

Bayan juyin mulkin 2013 a Masar ne aka aiyana kungiyar 'Yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar ta'adda a Masar.

 


News Source:   ()