Yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa a Sudan, wanda ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, ya tilasta wa fiye da mutane milyan 3 neman mafaka a ƙasashen maƙwabta ciki har da Chadi da Habasha da Sudan ta kudu da Libya da kuma Somalia ko da ya ke Masar na matsayin gida ga ɗimbin ƴan gudun hijirar na Sudan.
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Masar, ta ce yanzu haka akwai ƴan gudun hijirar Sudan dubu 546 da aka yiwa rijista, yayin da wasu da dama yanzu haka ke dakon ayi musu rijista.
Majalisar ɗinkin duniyar ta bayyana cewa miliyoyin ƴan gudun hijirar ta Sudan na tsananin buƙatar agajin jinƙai kama daga abinci da magunguna.
Tun a watan Aprilun 2023 ne yaƙi ya ɓarke a Sudan tsakanin Sojin gwamnati da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF yakin da ke matsayin mafi muni da ƙasar ta gani bayan makamancinsa a shekarun 2000 da ya tagayyara miliyoyin jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI