Yarjejeniyar wadda aka yiwa laƙabi da CFA da aka shafe fiye da shekaru 10 ana taƙaddama akanta, a Lahadin da ta gabata ne ta fara aiki wadda ta ƙunshi ƙasashe 10 da gaɓar kogin na Nilu ya ratsa su, za ta bayar da dama ga ƙasashen iya gudanar da gine-ginensu ko kuma ayyukan ci gaba a tsakar kogin ko da ba tare da izinin Masar ba, wadda ta cikinta ne ruwan kogin ke kwaranyowa.
Ƙarƙashin wannan yarjejeniya Habasha ba ta da wata togaciya game da shirinta na ginin madatsar ruwa a tsakar tekun wanda zai bata damar samar da tashar lantarki mafi girma a Afrika.
Yayin wani zaman taro da ƙasashen yankin kogin na Nilu suka gudanar a Uganda ƙarƙashin jagorancin Habasha ne aka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar duk da cewa ba a ga wakilcin ƙasashen Masar da Sudan ba.
Duk da yadda Habasha ta nutsa kuɗi har dalar Amurka biliyan 4 wajen ginin madatsar ruwan ta tsakar kogin Nilu, Masar na kallon wannan yarjejeniya a matsayin barazana gareta lura da cewa fiye da kashi 90 ba ruwan da ta ke samu na fitowa ne daga kogin na Nilu.
Wata sanarwa da ƙungiyar ƙasashen yankin kogin na Nilu ta fitar ta sanar da ɗage taron mambobinta da ta tsara gudanarwa ranar 17 ga watan nan a Uganda sai zuwa shekara mai kamawa.
\
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI