Dakarun ruwan na Masar da Faransa sun gudanar da atisayen "2021 Ramses" a tekun Baharul Ahmar.
Kakakin Rundunar Sojin Masar Kanal Tamir Al-Rifa ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Facebook cewa, a atisayen an yi amfani da jirgin ruwan yaki na Rundunar Sojin Ruwan Masar mai suna "Sejem Al-Fatih" da na Rundunar Sojin Ruwan Faransa mai suna "Charles de Gaulle" mai daukar jiragen sama.
Rifai ya kara da cewa, atisayen ya amfani dukkan bangarorin 2 ta fuskar samun horo da dama.
A gefe guda, Rifai ya kuma cewa, a lokacin da ake gudanar da atisayen "2021 Ramses", an kuma gudanar da wani atisayen na sojojin sama a wani sansanin sojin saman Masar da aka ki bayyanawa a ina yake.
Sanarwar ta kuma ce, atisayen da aka gudanar da manufar hada kai tsakanin dakarun Masar da Faransa, ana kuma da manufar kare manufofin kasashen 2 tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kan iyakokinsu.