
Shugabanin biyu sun tattauna kai tsaye kan batutuwan da suka shafi makomar Chadi da Burkina Faso da duba yiyuwar samar da kwamitin hadin gwiwa da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Sahel biyu.
Pingwendé Gilbert Ouédraogo, Ministan Sadarwa na Burkina Faso ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun yi maraba da haduwar ra'ayoyinsu kan manyan batutuwan da suka shafi makomar ƙasashensu, musamman neman samun 'yancin cin gashin kai na gaskiya, yaƙi da sabon tsarin mulkin mallaka, da samar da ingantacciyar damar da za a iya samu a fannonin.
Marshal Mahamat Idriss Deby Itno ya je wurin tunawa da kyaftin Thomas Sankara inda ya ajiye wata fure a wurin ga mutumen da taka muhimiyar rawa a juyin juya halin Burkina Faso wanda ya yi tasiri a tafiyar kasashen yankin na Sahel.
Marshal Mahamat Idriss Deby Itno da babbar murya ya na mai cewa: "Burkina Faso da Chadi suna da dogon tarihi a fanoni da dama,wanda ya kuma dace a karfafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI