Mamadi Doumbouya, ya daukaka kansa zuwa matsayin janar na soja

Mamadi Doumbouya, ya daukaka kansa zuwa matsayin janar na soja

A baya,musamman a watan Janairun shekarar 2024 ne shugaban sojan ya daukaka kansa zuwa mukamin laftanar Janar yayin da ya bayyana cewa gwamnatin mulkin sojan ba za ta cika alkawarin da ta yi na mika mulki ga zababbun farar hula nan da karshen shekara ba.

Janar  Mamadi Doumbouya, Shugaban kasar Guinee Janar Mamadi Doumbouya, Shugaban kasar Guinee © AFP

A cikin wata doka da yammacin jiya Juma'a, an samun labari ta yada magoya bayansa suka bukaci ya tsaya takarar shugaban kasa a yan lokuta bayan ba shi lambar yabo ta Grand Cross of the National Order of Colatier, wanda shi ne mafi girma a kasar.

Cellou Dalein Diallo, tsohon Firaminista kuma jagoran yan adawa Cellou Dalein Diallo, tsohon Firaminista kuma jagoran yan adawa © AFP/Sia Kambou

Wannan ya kasance saboda "kokarin da yake yi akai-akai don inganta haɗin kan zamantakewa da haɗin gwiwa tsakanin mutane".

Doumbouya na daya daga cikin hafsoshi da dama da suka kwace mulki a yammacin Afirka tun daga shekarar 2020, tare da wasu shugabannin sojoji a Mali, Burkina Faso da Nijar.

Doumbouya ya jagoranci ci gaba da murkushe 'yan adawa, inda ake tsare da jagororin adawa da dama, da gurfanar da su gaban kotu ko kuma tilasta musu yin gudun hijira.

Duk da dimbin albarkatun kasa da take da su, Guinea ta kasance kasa mai fama da talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)