Mali,Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa za su ƙaddamar da sabon fasfonsu

Mali,Burkina Faso da Nijar sun sanar da cewa za su ƙaddamar da sabon fasfonsu

Shugaban gwamnatin sojin Mali, janar Assimi Goita,a gidan talabijen na kasar ya ce sabon fasfon zai fara aiki ranar 29 ga watan Janairun 2025, sai dai tsohon fasfonsu zai ci gaba da aiki har zuwa ranar da wa’adin amfani da shi ya ƙare.

Janar Assimi ya ƙara da cewa al’ummar ƙasashen 3 za su iya kai fasfonsu mai tambarin ECOWAS domin a sauya musu da sabon fasfon da suka samar.

Shugaban majalisar sojin Mali Janar Assimi Goita Shugaban majalisar sojin Mali Janar Assimi Goita © Facebook / Présidence du Mali (capture d'écran)

Ƙasashen Sahel ɗin sun kuma sanar da cewa za su haɗa karfi da karfe domin samar da rundunar tsaro mai dauke da dakaru 5,000, ta yadda za su taimakawa kawunansu wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankula da suka addabesu tsawon shekaru.

Bayan kwace mulkin daga hannun fararen hula tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, shugabannin ƙasashen 3 na yammacin Afrika, wato Mali, Burkina Faso da Nijar, sun haɗu domin kafa sabuwar ƙungiyar haɗakar ƙasashensu.

A ranar 28 ga janairun shekarar 2024 da ta gabata, ƙasashen 3 suka sanar da ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, wacce suka zarga da zama ‘yar amshin shatan Faransa tare da gazawa wajen taimaka musu a yaƙin da suke da ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)