Mali ta sallami jakadiyar ƙasar Sweden daga ƙasar

Mali ta sallami jakadiyar ƙasar Sweden daga ƙasar

Korar Jakadiyar Kristina Kuhnel na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Malin ta sanar da yanke duk wata alaƙa tsakaninta da Ukraine.

Gwamnatin Sojin Mali ta zargi jakadiyar da yunkurin shigar da siyasa da kuma yaɗa ƙarya kan abinda ya shafi alaƙarta da ƙasahen ketare musamman Rasha.

Tun farko dai Mali ta zargi babban jakadan Ukraine a ƙasar da yunƙurin rura wutar ta’adddanci bayan da ya shaida cewa Ukraine ta baiwa ƴan tawayen Abzinawa taimako wajen hallaka sojoji Wagner da kuma sojojin ƙasar sama da 50 a watan Yulin da ya gabata.

Sai dai kuma tun a wancan lokaci gwamnatin Ukraine a hukumance ta musanta wannan iƙirari da kuma zargi a lokaci guda.

Sweden na cikin ƙasashe na gaba-gaba da ke baiwa Mali tallafin kuɗaɗe don yaƙi da ta’addanci, inda bayanai ke cewa cikin shekaru 10 da suka gabata, Mali ta karɓi tallafin kuɗaɗe har dala miliyan 300 daga Sweden ɗin.

Tun bayan da aka kifar da gwamnatin farar hula a Mali, sojoji suka fara yanke alaƙar diplomasiyya da ƙasashen turawa duk a bisa zarginsu da hannu a aikata ta’addancin da ke faruwa a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)