Mali ta saki wasu jami'ai 3 na kamfanin hakar zinare daga Australia

Mali ta saki wasu jami'ai 3 na kamfanin hakar zinare daga Australia

An kama mutanen uku ne a cikin wannan watan bayan tafiya zuwa Bamako babban birnin kasar domin yin shawarwarin da suka saba yi da gwamnatin mulkin soja. Madadin haka, babban jami'in zartarwa na Birtania Terence Holohan da abokan aikinsa guda biyu an "kama su ba zato ba tsammani" don amsa tambayoyi.

Majiyar shari'a ta ce "An saki shugabannin uku na kamfanin Australia da aka kama bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu."

 Tun bayan da suka karbe mulki, shugabannin sojojin Mali sun sha alwashin dakile kudaden shigar da ake samu daga kamfanonin kasashen waje da ke aiki a kasar. Resolute dai na da kashi 80 cikin 100 na wani reshen da ya mallaki mahakar ma'adinan arewa maso yammacin garin Syama, inda gwamnatin Mali ke rike da sauran kashi 20 cikin 100, a cewar shafin yanar gizon kamfanin.

Wasu daga cikin masu hako zinare Wasu daga cikin masu hako zinare © AP - Marc Hofer

 Wani jami'in kasar Mali daga mahakar ma'adinan Syama ya tabbatar da cewa "hakika an sako shugaban da sauran jami'an kamfanin biyu". Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin 'yan watannin nan da ake tsare da ma'aikatan wani kamfanin hakar ma'adinai na kasashen waje.

Biyan dala miliyan 160 wani gagarumin cikas ne ga Kamfanin Resolute, wanda bisa ga bayanan kudi a halin yanzu yana da tsabar kudi dala miliyan 157.

Kamfanin Resolute ya ce za ya biya gwamnatin Mali dala miliyan 80 daga cikin "ajiyar kudi", tare da kara biyan dala miliyan 80 a cikin "watanni masu zuwa".

masu aikin hako zinare masu aikin hako zinare REUTERS - Francis Kokoroko

Duk da kasancewar kasar Mali na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba wajen samar da zinare a nahiyar Afirka, ita ma kasar Mali na daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.

 Kasar ta Mali da ke Afrika ta Yamma dai na fama da rikicin siyasa, tsaro da tattalin arziki, kuma tun a shekara ta 2012 take fafatawa da kungiyoyin Al-Qaeda da na IS, da kuma 'yan awaren arewacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)