Tashar ta TV5 mai yaɗa shirye-shiryenta da harshen faransanci ita da kanta da sanar da wannan hukunci na mahukuntan na Mali ga kamfanin dillancin labarai na AFP.
Sanarwar da Sojin na Mali suka fitar sun ce hukuncin zai fara aiki nan ta ke wato daga jiya 11 ga watan Stumban da muke ciki.
Hukumomin na sojin na Mali sun zargin wannan tashar da bada labarai da suka sabawa dokokin ƙasar.
Da samun wannan labari, kungiyoyi kare hakokin ƴan jarida ta kasa da kasa wato RSF da babbar murya ta na mai bayyana damuwa da kuma takaici ganin ta yada hukumomin sojin Mali suka aiwatar da wannan mataki ba tare da tuntuba ba.
Matakin shi ne na dakatar da watsa shirye-shiryen wannan tasha na tsawon watanni uku bisa zargin su da rashin daidaito a fannin yada labarai biyo bayan farmaki dakarun kasar a yankin Tinzaoutaene.
Hukumar Kula da Sadarwa ta kasar ta Mali (HAC) ta soki tashar ta TV5 Monde da bayar da rahoto a ranar 25 ga Agusta, a cikin labarun ta na Afirka, mutuwar akalla fararen hula goma sha biyar a harin da jirage marasa matuka a Tinzaouatène da ke arewacin kasar ta Mali.
Tashar ta TV5 a cikin wata sanarwa ta na mai nadama da kuma nuna mamakin ta na ganin hukumar kula da sadarwa ta kasar ta Mali ba ta nemi jin ko ta bakin masu wakiltar wannan tashar ba kafin daukar irin wannan mataki .
Ko a ƴan shekarun da suka gabata, ƴan lokuta bayan juyin mulkin sojojin kasar an dakatar da kafofin watsa labarai da yawa da kafafan yada labarai na France24 da kuma Radio France Internationale (RFI).
Haka zalika Sojin na Mali sun kuma dakatar da France2 a farkon shekarar 2024, kafin LCI ta fuskanci irin wannan makoma a karshen watan Agusta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI