Duk da cewa auren jinsi na fuskantar ƙyama a Mali amma har yanzu babu ko mutum guda da aka taɓa kamawa ko kuma yankewa hukuncin kan auren na Jinsi lura da yadda al’adu da addini ke da ƙarfi a ƙasar mai rinjayen Musulmi.
Yanzu haka dai wannan ƙudiri na buƙatar sa hannun shugabannin mulkin Sojin ƙasar gabanin zama doka sai dai ministan shari’a na Malin Mamadou Kassougue ya bayyana cewa dukkanin wanda aka samu da ɗabi’ar ta auren jinsi kai tsaye zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Bayanai sun ce yayin zaman kaɗa ƙuri’ar mambobin majalisar 132 ne suka amince da ƙudirin yatinda mutum guda yaƙi amincewa.
Sanarwar da majalisar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ruwaito Kassougue na cewa bisa taimakon ubangiji dokar za ta yi tasiri domin baza su bar ɗabi’ar ta lalata musu kyawawan al’adunsu ba.
Wannan sabuwar doka ta Mali ya nuna yadda ta bi sahun ƙasashen Mauritania da Somalia da Sudan wajen haramta auren na jinsi da zuwa yanzu ƙasashen Afrika aƙalla 30 suka ƙaddamar da haramcin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI