Mali, Burkina Faso da Nijar sun janye buƙatar visa tsakaninsu da ECOWAS

Mali, Burkina Faso da Nijar sun janye buƙatar visa tsakaninsu da ECOWAS

Wata sanarwar haɗakar ƙasashen 3 da ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya fitar a Asabar ɗin da ta gabata ta ce a yanzu al’ummomin ƙasashen ECOWAS 12 ka iya shiga ƙasashen 3 ba tare da neman visar shiga ba.

Gabanin sanar da ficewa daga cikin ECOWAS, gamayyar ƙasashen na yammacin Afrika 15 ba sa buƙatar visa a tsakaninsu gabanin ƙetare iyakokinsu, sai dai ficewar wannan ƙasashe ya sanya fargabar yiwuwar buƙatar visa, ko da ya ke dama sai a watan Janairun shekara mai kamawa ne wa’adin ficewarsu daga ƙungiyar zai cika a hukumance.

Ƙasashen 3 da dukkaninsu Faransa ta yiwa mulkin mallaka kuma yanzu Sojoji ke mulkarsu wanda ya kawo ƙarshen alaƙarsu da uwar goyonsu sun ce hatta motocin ƴan kasuwa ko kuma na ɗaiɗaikun jama’a na zarrar shiga ƙasashen 3 ba tare da wani shinge ba.

Sai dai sun tsaurara matakai kan ƴan gudun hijira waɗanda suka ce shigar ƴan gudun hijira ƙasashen 3 na buƙatar cikakkun bayanai da kuma tantancewa.

Wannan mataki na zuwa ne a wani yanayi na ƙasashen 3 ko kuma haɗakar ta AES ke nanata ƙudirin ƙin amincewa ko kuma amsa kiraye-kirayen buƙatar komawa cikin ECOWAS.

Dukkanin ƙasashen na Sahel 3 dai na fama da matsalolin tsaro daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da kuma ƴan tawaye a wasu yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)