Mali, Burkina Fasa da Nijar na zargin ɗan jaridar Faransa da goyon bayan ta'addanci

Mali, Burkina Fasa da Nijar na zargin ɗan jaridar Faransa da goyon bayan ta'addanci

Nasr, ma’aikacin tashar talabijin ta France 24 ne, kuma masanin tsaro, wanda a kullum ya ke sharhi a kan ayyukan ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi da su ka samo asali daga Mali a shekarar 2012, su ka kuma bazu zuwa yankin Sahel na yammacin nahiyar Afrika.

A ranar 17 ga watan Satumba, ya yi wani dogon sharhi a kan wani harin dasa-bambam da mayaƙa masu ikirarin jihadi su kai wasu mahimman wurare a babban birnin Mali, Bamako, kuma bayan hare-haren, an kama sunansa a kafafen yaɗa labarai da dama.

Masu gabatar da ƙarar, waɗanda su ka fito daga ɓangarorin shari’a da su ka ƙware a kan abin da ya shafi ta’adddanci a Mali, Burkina Faso da Nijar, sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa da aka watsa a tashoshin talabijin a daren Laraba.

Sun zargi Nasr da yin kalaman da su ke nuna yana taimakawa wajen yaɗa manufofin ta’addanci da kuma nuna goyon baya ga ayyukan mayaƙa masu ikirarin jihadi, musamman hare-haren kwanan nan a Bamako da kuma garin Djibo na Burkina Faso.

Nasr, wanda ke zaune a Faransa ya wallafa a shafinsa na X cewa ba shi da abin da zai ce a game da wannan al’amari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)