Majalisar Larabawa ta yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da su yi duk mai yiwuwa don dakatar da zartar da hukuncin kisa da kotun Masar ta yankewa wasu shugabannin Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi su 12.
Majalisar wadda Tsohon Shugaban Masar Munsif Al-Marzuki ya ke jagoranta ta bayyana cewa, suna suka da la'antar wannan hukunci da kotun Masar ta yankewa shugabannin 'Yan Uwa Musulmi.
Sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkokin dan adam na kasa da kasa da su dakatar da zartar da wannan hukunci.