Wasu ƴan majalisun dokokin Kenyan ne suka gabatar da ƙudirin tsige mataimakin shugaban ƙasar, inda tuni suka fara zama kan kudurin a ranar Talata, al’amari da ke kara fito da rashin jituwa tsakanin ƴanƴan jam’iyyar mai mulki.
Tun a watan Maris ne siyasar ƙasar da ke gabashin Afirka ta fada cikin rudani, sakamakon kazamin zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ƙarin haraji da matasan ƙasar suka gudanar.
Ana zargin Gachagua da yi wa gwamnati zagon ƙasa, da cikin cin hanci da rashawa da rashin biyayya da gudanar da siyasar kabilanci da wasu laifuffuka.
Ƴan majalisar wakilai 291 ne suka rattaba hannu kan amincewa da ƙudirin, wanda ya zarce mafi karancin da aka bukata na wakilai 117.
Kakakin majalisar dokokin ƙasar, Moses Wetangula, ya ce kudirin, wanda ɗan majalisa Mutuse Eckomas Mwengi, daga jam'iyyar mai mulki ya gabatar -- ya cika dukkan sharuddan tsarin mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI