
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce al’ummar Sudan na tsananin buƙatar agajin jinƙai dalilin da ya sanya ƙara yawan kuɗaɗen da ake buƙata na wannan tallafi da aƙalla kashi 40 kan ainahin kuɗaɗen da ta buƙata da farko.
A cewar Majalisar, ɗimbin ƴan Sudan ne suka rasa matsugunansu bayan da yaƙin ya tagayyarasu cike da tarin matsaloli ciki har da ƙarancin abinci da ya haddasa matsananciyar yunwa da kuma ƙarancin magunguna kula da masu fama da rashin lafiya.
Buƙatar wannan kuɗaɗe na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Donald Trump na Amurka ya katse tallafin da bisa al’ada ƙasar ta saba bayarwa don ceto rayukan jama’a a sassan Duniya.
Sai dai majalisar ta ce neman tallafin ya zama dole ne duba da yadda aka share watanni 22 ana gwabza wannan yaƙi tsakanin jami’an sojin ƙasar da dakarun RSF wanda ya tagayyara kaso mai yawa na jama’ar ƙasar tare da jefa su cikin mawuyacin hali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI