Majalisar Dokokin Libiya ta mayar da martani ga Masar

Majalisar Dokokin Libiya ta mayar da martani ga Majalisar Dokokin Masar da ta amince da wani kudirin doka da ya ba wa Abdulfatah Al-Sisi ikon tura sojoji Libiya".

Sanarwar da aka fitar daga Majalisar Dokokin Libiya da ke Tarabulus ta ce "Muna adawa da wannan hukunci wanda wasu da ba su da halasci da ke da alaka da majalisar dokoki ta karya da ke Tobruk suka bayyana gayyatar Masar."

Sanarwar ta yi kira da a gaggauta sukar wannan mataki na Majalisar Dokokin Masar, kuma gwamnatin Libiya za ta yi amfani da dukkan damar da ta ke hannunta don mayar da martani ga wannan mataki.

Sanarwar ta ce "Libiya ba ta yin wata barazana ga zaman lafiyar Masar. Majalisar Dokokin Masar sai ta shirya nade kafar wandonta saboda barazanar soji."

Ministan Harkokin Cikin Gida na Libiya Fethi Basaga ya ce wannan dama da Majalisar Dokokin Masar ta ba Al-Sisi kamar aiyana yaki ga Libiya ne.

Sanarwar da Basaga ya fitar ta shafinsa na Twitter ta ce

"Wannan amincewa da Majalisar Dokokin MAsar ta yi na kasar ta tura dakrunta zuwa yammacin Libiya aiyana yaki ne ga kasar ta Libiya. Kuma hakan ya karya dokokin Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Larabawa."


News Source:   ()