Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa matakin hukunta masu laifi a Guinea

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa matakin hukunta masu laifi a Guinea

Sanarwar mai dauke da sanya hannun babban Kwamishinan kare hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya jaddada muhimmancin ci gaba da yin aiki da doka da oda musamman bayan gano mutanen da ke da hannun a laifukan da suka jibanci cin zarrafi.

Bayan kusan shekaru 15 da aikata wadanan laifuka, lokaci ne da kotu za ta bayyana gaskiya a kai,kuma wadanda abin ya shafa, wadanda suka tsira da iyalansu suna da hakkin sanin abinda ya faru.

Moussa Dadis Camara. Moussa Dadis Camara. (Photo : Laurent Correau / RFI)

Baya ga aiwatar da hukuncin kotun, babban kwamishina yana ganin yana da matukar muhimmanci ga gwamnatin Guinea ta tantance makomar duk mutanen da suka bace da kuma tabbatar da cewa wadanda ke da hannu wajen bacewar mutane da laifukan da suka aikata.

Har ila yau, ta nanata cewa wadanda abin ya shafa da kuma 'yan uwansu na da 'yancin cin gajiyar "cikakkiyar tallafi daga hukumomi wannan kasar.

Tsohon Shugaban majalisar Sojin Guinea Moussa Dadis Camara, Tsohon Shugaban majalisar Sojin Guinea Moussa Dadis Camara, © AFP/Seyllou

 Indan aka yi tuni, a ranar 28 ga Satumba, 2009, akalla mutane 156 ne aka kashe ta hanyar harbin bindiga, wuka, adduna, tare da raunata daruruwan wasu, a sakamakon murkushe masu zanga-zangar adawa a wani filin wasa na Conakry da kewaye.

Akalla mata 109 aka yiwa fyade. An ci gaba da cin zarafin mata da aka yi garkuwa da su da kuma azabtar da fursunonin da ake tsare da su tsawon kwanaki da dama.

Rahoton bincike na nuni cewa an binne wasu da dama da abin ya rutsa da su a cikin manyan kaburbura.

Tsohon shugaban sojin lokacin Moussa Dadis Camara ne ke da alhakin manyan laifuka da suka hada da kisan kai, cin zarafin mata, azabtarwa, garkuwa da mutane da kuma,an yanke wa wasu mutane bakwai hukuncin daurin rai da rai a gidan yari biyo bayan shari’ar da aka  shafe kusan shekaru biyu ana yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)