Jagoran juyin mulki kuma sabon Shugaban Kasar Mali Assimi Goita ya nada Choguel Maiga a matsayin Firaminista.
Kamfanin dillancin labarai na Amap da ke Mali ya sanar da cewa, Goita ya nada Choguel Maiga na Hadin Kan 'Yan adawar M5-RFP a matsayin Firaminista.
Maiga mai shekaru 63 kuma wanda ya kafa jam'iyyar Gwagwarmayar Kishin Kasa, ya rike mukamin Ministan Kasuwanci da Masana'antu a tsakanin 2002-2007 inda a tsakanin 2015-2016 kuma ya rike mukamin Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki.
Maiga na daga cikin wadanda suka yi shuhura wajen gudanar da zanga-zangar da ta biyo bayan murabus din tsohon Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita.