Mai yiwuwa ƴan ƙasashen AES su buƙaci fasfo kafin su shiga makwaftansu na ECOWAS

Mai yiwuwa ƴan ƙasashen AES su buƙaci fasfo kafin su shiga makwaftansu na ECOWAS

A wata ganawa da RFI Hausa a Abuja, ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar  ya ce daga cikin wahalhalun da ECOWAS ke guje wa al’ummomin waɗannan ƙasashe, akwai batun fasfo, wanda kafin a kai ga samun masalahar sauya su zuwa na ƙasasashen AES ba za a ji da daɗi ba.

Tuggar ya ce za a kashe kuɗaɗe masu yawa wajen buga fasfo duba da cewa na zamani ne ake yaye yanzu, kuma abin da hakan ke nufi shi ne zai yi wuya wani wanda ba  ɗan ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS ya shiga ba tare da fasfo ba idan ba a daidaita  ba.

Ya kawo misali da ofishin kula da lafiya na ƙungiyar ECOWAS da ke birnin Ouagadougou na Burkina Faso, wato WAHU, inda ya ce ƙarshen ta sai dai a ɗauke shi daga birnin, kuma yawancin ma’aikata ƴan ƙasar su yi asarar guraben ayyukansu.

Ministan harkokin wajen na Najeriya ya ce akasin yadda aka yi ta zargin babu wani abin da ECOWAS ke yi don sasantawa da waɗannan ƙasashe, Najeriya ta zaƙe a kan sulhuntawa, inda har ta aike da kwamiti wadannan ƙasashen don shawo kan shugabanninsu su dawo amma  ba su amince ba.

Idan ba  a manta ba, sai da kungiyar ECOWAS ta bai wa ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ƙarin watanni 6 su sake nazari a kan matakinsu, amma su ka yi kunnen uwar shegu da shi.

Sai dai Tuggar ya ce har yanzu ƙofa a buɗe ta ke ga waɗannan jagororin gwamnatin soji idan har su na sso a ci gaba da Tarraya a cikin ECOWAS.

A watan Janairun wannan shekarar ce kasashen uku suka sanar da ficewarsu daga kungiyar ECOWAS wacce suka zarga da zama ‘yar amshin shatan Faransa, don haka suka samar da ta su kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)