
Kahn na shirin ganawa da hukumomin Congo, inda ya fara da shugaban ƙasar, Félix Tshisekedi, da sauran manyan mukarraban gwamnati.
Wannan na zuwa ne, yayin da ƙasar ke fama da munana hare-haren /yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan dakarun Rwanda, musamman a gabashin ƙasar.
A cewar ƙwararu na Majalisar Ɗinkin Duniya, M23 na samun goyon bayan sojojin Rwanda kusan 4,000.
A cikin 'yan makonnin da suka gabata, ƙungiyar ta ƙwace ikon wasu manyan garuruwa biyu a Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Rwanda dai na ci gaba da musanta zzarge-zargen da ake mata na taimakawa 'yan tawayen M23.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI