Mahukuntan Kenya sun ɗau matakan hana tasirin yajin aikin ma'aikatan filin jirgi

Mahukuntan Kenya sun ɗau matakan hana tasirin yajin aikin ma'aikatan filin jirgi

Hukumar kula da sufurin jiragen saman ta Kenya ta ce ko da ƙungiyar ma'aikatan ta aiwatar da aniyar ta ta tsunduma yajin aikin ba lallai ya yi tasiri kamar yadda ta ke hasashe ba.

Ƙungiyar ma’aikatan filayen jiragen sama na Kenya ta sha alwashin shiga yajin aikin ne, kan yarjejeniyar da ta yi zargin ta sayar da babban Filin Jirgin Saman kasar na Jomo Kenyatta ne ga ƙasar India, ta yadda harkokin tafiyarwa filin kacokan za ta koma hannun New Delhi.

Ma’aikatan filayen jiragen saman, sun ce muddin hakan ta tabbata, to fa  babu makawa zai kai ga rasa guraben ayyukan da  dama daga cikinusu, waɗanda kuma za a maye gurbinsu da wasu sabbin ma’aikkatan kuma baƙi Indiyawa.

Tuni dai gwamnatin Kenya ta musanta zargin shirin sayar da filin jiragen saman na Jomo Kenyatta, inda ta ce ta na neman kulla yarjejeniyar ce kawai domin bunƙasa katafaren filin jiragen saman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)