A ɓangare guda bayanai sun ce kogin Logone ya yi tumbatsa mafi ƙololuwa da ba a ga irinta cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata ba, wanda ya sanya matakin da ya sanya fargabar sake tsanantar ambaliyar ƙasar wadda kawo yanzu ta hallaka mutane 576 tare da raba wasu miliyan 1 da dubu 900 da matsugunansu tun bayan farowarta a watan Yulin da ya gabata.
Masana sun yi gargaɗin cewa wasu sassa na Chadi ka iya fuskantar zabtarewar laka ƙari kan ambaliyar da ake ci gaba da gani tsawon makwanni.
Ƙasashe da dama a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika ne suka yi fam ada ambaliyar ruwa a damunar bana, sai dai halin da ake ciki a Chadi ya fi ko’ina tsananta lura da yadda matsalar ta shafi miliyoyin iyalai.
Shugabar hukumar kula da albarkatun ruwa ta Chadi Sakine Youssouf ta ce tumbatsar kogin Logone ya wuce yadda ake tsammani inda a jiya Laraba ya kai mita 8.18 fiye da yadda aka yi tsammanin tumbatsar shi.
Tuni dai Firaminista Maye Halina ya jagoranci wani taron gaggawa na masu ruwa da tsaki don ɗaukar matakan da za su baiwa jama’a kariya daga ƙaƙƙarfar ambaliyar da ake hasashe da kuma wadda tuni ta shafi yankuna 17 cikin 23 da ƙasar ke da su ciki har da fadar gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI