An sanar da cewa wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a jihar Zamfara dake Najeriya inda suka kashe mutum 23.
Kamar yadda kafafen yada labaran cikin gida suka rawaito mahara dauke da makamai saman babura sun kai hari a kauyen Ruwan Tofa inda suka kashe mutum 23.
Mai magana da yawon ýan sandan jihar Muhammad Shehu ya bayyana cewa tuni an dauki mataki domin an tura jami'an tsaro a yankin da lamarin ya afku.