An kai wani sabon hari a jihar Kaduna dake Najeriya inda aka kashe mutum 13.
Shugaban yan sandan jihar Samuel Aruwan ya bayyana cewa an kai hare hare a yankunan Zangon Kataf, Chikun da Karu.
Aruwan, ya bayyana cewa a harin da wasu da ba'a san ko su wanene suka jau mutum 13 sun rasa rayukansu inda wasu 7 suka raunana.
Ya kuma kara da cewa maharan sun kone gidaje 56 da babura 16 lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gudajensu sabili da tsoro.
Sabili da kai hare hare da babura an saka dokar hana amfani da babura a wasu jahohin kasar na Najeriya.
A yan kwanakin da suka gabata an kai harin da ya yi sanadiyar rayukan mutun 19.