Deby ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci yankin da mayakan boko haram suka hallaka masa sojoji 40.
Shugaban wanda ya yi zargin rashin hadin kai tsakanin sojojin dake yaki da 'yan ta'addan ya ce wannan matsalar ce ke haifar da koma baya a yakin da suke yi. Ya zuwa yanzu dai kasashen dake da sojoji a rundunar ba su ce komai a kai ba. Kasashen dake da sojoji a cikin wannan rundunar dake yaki da mayakan boko haram sun hada da Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Benin.
Wasu daga cikin dakarun Chadi a yankin tafkin Chadi © APWannan sanarwar manema labarai na zuwa ne a lokacin da shugaban kasar Mahamat Idriss Deby ya kwashe mako guda yana fagen daga, wanda aka bayyana a matsayin jagoran yaki da ke jagorantar farmakin da ake kira Haskanite, wanda aka kaddamar bayan mutuwar sojojin Chadi kusan 40.
Tun a shekarar 1994, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Force (MMF) ta hada kasashen Chadi, Kamaru, Benin, Najeriya da Nijar.
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno AFP - DENIS SASSOU GUEIPEURKuma asali an kafa ta ne don yakar ‘yan fashi, daga baya ta rikide zuwa hadin gwiwar yaki da ta’addanci.
Lura cewa Nijar ta dakatar da shiga cikin rundunar hadin gwiwa bayan juyin mulki na watan Yulin 2023,wasu kasashen na ci gaba da girke dakarun su a kan iyakoki, bayan sauye-sauyen dangantaka da Najeriya, gwamnatin mulkin soja ta ce a shirye ta ke, a karshen watan Agusta, don ci gaba da aiki da sauren kasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI