Mahama ya kafa kwamitin binciken gwamnati mai barin gado kan laifukan rashawa

Mahama ya kafa kwamitin binciken gwamnati mai barin gado kan laifukan rashawa

Dan Majalisar dokoki mai ci da ke jagorantar kwamitin sa ido kan manyan jami’an gwamnatin Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwah ne ke jagorantar tawagar masu binciken zarge-zargen laifukan na rashawa, wanda ko a watannin baya-bayan nan sai da ya taɓa kwarmata wasu daga cikin laifukan da ake zargin an aikata a ƙarƙashin gwamnatin da ke shirin miƙa mulki.

Sauran mambobin tawagar gwamnatin Ghanan mai bincike kan laifukan cin hanci da rashawa sun haɗa da, tsohon jami’in Ɗan Sanda, da wani babban Lauya, da kuma ɗan jarida mai binciken ƙwaƙwaf ko kuma ƙwalam ta ƙoƙi mai ganin man dutse.

Sauran sun haɗa da tsohon babban jami’in binciken kudi na gwamnatin Ghanan Daniel Dumelovo, wanda a baya aka cire shi daga muƙamin, saboda wallafa sakamakon wani bincike da yayi a kan wata badaƙalar kuɗi da aka aikata a zamanin gwamnatin Nana Akufo-Addo mai shirin ƙarewa.

Yaƙi da laifukan cin hanci da rashawa gami da ƙwato kuɗaɗen da aka yi kwanciyar magirbi a kansu na daga cikin manyan alƙawuran da John Mahama  ya yi, yayin yakin neman sake zaɓensa a matsayin shugaban Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)