Kwanaki 2 bayan da Mahama ya kama aiki a ranar 9 ga watan da muke ciki na Janairu ne, Mahama ya shigar da wannan shiri cikin manufofinsa kamar yadda ya ke ƙunshe a gazette.
Ma’aikatun wannan mataki ya shafa sun ƙunshi ma’aikatar yaɗa labarai da tsaftar muhalli da albarkatun ruwa sai kuma ma’aikatar tsaron ƙasa kana ma’aikatar bunƙasa sufurin jiragen ƙasa sai kuma ma’aikatar da ke kula da harkokin majalisa.
Sauran sun ƙunshi ma’aikatar da ke kula da sassan gwamnati kana ma’aikatar kula da masarautu da harkokin addini.
Bayanai sun ce kusan dukkanin masarautun da wannan mataki ya shafa an samar da su ne ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata ta tsohon shugaba Nana Akufo-Addo.
Ku latsa alamar sauti don sauraron rahoto kan wannan mataki tare da wakilinmu na Ghana Abdallah Sham'un Baƙo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI