A Malawi da ke Gabashin Afirka, madugun 'yan adawa Lazarus Chakwera ya lashe zaben Shugaban Kasar da aka gudanar.
Sanarwar da Hukumar Zabe ta Kasa ta Malawi ta fitar ta ce Chakwera mai shekaru 65 dan jam'iyyar adawa da MCP ya samu kaso 58,6 na kuri'un da aka jefa inda ya zama wanda ya yi nasarar lashe zaben.
Sanarwar ta ce Shugaban Kasar Mai ci na jam'iyyar DPP Peter Mutharika ya samu kaso 39,4, sai dan takarar jam'iyyar DMP Saulos Chilima da ya samu kaso 0,73.
Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Chifundo Kachale ya ce sakamakon yadda Chakwera ya samu kuri'un da ake bukata, shi ne ya lashe zaben Shugaban Kasar.
Kotun Kolin Malawi ta soke zaben Shugaban kasar da aka yi a ranar 21 ga watan Mayun 2019 sakamakon tafka magudi da ta ce an yi.
A wannan zaben, Shugaban Kasar Mai Ci na jam'iyyar DPP Mutharika ne ya samu kaso 38,57 kuma aka bayyana a matsayin wanda ya yi nasara.
Madugun 'yan adawa tsohon Pasto Chakwera kuma ya samu kaso 35,4 inda dan takarar DMO Chilima kuma ya samu kaso 20,2.