Madugun adawar Somaliland Abdirahman Cirro ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

Madugun adawar Somaliland Abdirahman Cirro ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

Wata sanarwa da hukumar zaɓen yankin na Somaliland ta fitar a yau Talata ne ta bayyana Abdirahman Cirro a matsayin wanda ya lashe zaɓen wanda ya share hanyar samun sabuwar jam’iyya da za ta mulki yankin karon farko tun bayan ɓallewarsa daga Somalia.

Cirro wanda shi ne madugun jam’iyyar adawa ta Waddani da ke rajin samar da sauyi a siyasar yankin ta alƙawarta manya-manyan sauye-sauye matuƙar ta samu nasarar jagorantar yankin.

Shugaban hukumar zaɓen yankin na Somaliland Musa Hassan ya bayyana cewa Abdirahman Cirro ya lashe kashi 64 na ƙuri’un da aka kaɗa yayinda shugaba Bihi ya samu kashi 35.

Yankin na Somaliland mai yawan jama’a miliyan 6 tun a shekarar 1991 ne ya ɓalle daga Somalia sai dai har zuwa yanzu babu ko da ƙasa guda da ta amince da ƴancinsa, duk da cewa a baya-bayan nan ya ƙulla alaƙar kasuwanci da Habasha wadda za ta baiwa Addis Ababa damar amfani da gabar ruwan yankin.

Al’ummar yankin na Somaliland na fama da matsalar gaza iya bulaguro saboda rashin sahihin fasfo wanda ke tilasta musu iya balaguro zuwa sauran sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)