Ziyarar ta yau Litinin da ke zuwa bayan tsamin alaƙa tsakanin Faransar da Morocco wanda ya kaisu ga shafe tsawon shekaru suna takun saƙa kan batutuwa da dama.
Tun farko Sarkin Morocco Mohammed na VI ne ya aike da goron gayyata ga Macron wanda ya ce akwai fatan ƙasashen biyu su ajje banbancinsu a gefe tare da rungumar alaƙar da tun farko ta haɗasu don ƙarfafa alaƙarsu.
Rikici tsakanin Paris da Rabat ya samu asali ne bayan da Faransa ta bayyana matsayarta kan yankin na yammacin sahara da ake taƙaddama kansa tsakanin ƴan tawayen Polisario masu samun goyon bayan Algeria da kuma Moroccon.
Yankin na Yammacin Sahara wanda Spain ta yiwa mulkin mallaka da kuma ya shafe tsawon shekaru yana fafutukar samun ƴanci daga Morocco wadda ke kallonshi a matsayin mallakinta, a shekarar 2020 ya ayyana yaƙi da mahukuntan ƙasar don ƙwatar ƴanci.
A watan Yulin da ya gabata ne, shugaba Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga samar da ƴancin yankin da nufin wanzuwar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin biyu da kuma Algeria daga gefe, sai dai batun bai yiwa Morocco daɗi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI