Shugaba Macron ya yaba da Larbi Ben M'hidi, ya na mia cewa gwarzo ne dan kasar Aljeriya kuma daya daga cikin shugabannin FLN shida da suka kaddamar da tawaye a ranar 1 ga Nuwamba, 1954, sojojin Faransa da ke karkashin jagorancin Janar Aussaresses sun kashe shi.
Fadar ta Élysée ce ta fitar da wannan sanarwar ga manema labarai a yau a lokacin bikin cika shekaru 70 na tawaye na Nuwamba 1, 1954.
Wasu daga cikin shugabanin FLN na lokacin a Algeria Domaine publicSau da yawa 'yan uwansa suka gabatar da shi a matsayin gwarzo , an kashe shugaban FLN a shekara ta 1957 wanda Janar Paul Aussaresses ya kashe,sai dai a lokacin aka samu mabanbanta ra’ayoyin dangane da mutuwar sa.
A cikin sanarwar manema labarai, fadar shugaban kasar Faransa ta ba shi girmamawa, tare da tabbatar da cewa "sojojin Faransa da suka san shi ,sun yaba masa ganin kwarjininsa da jaruntakarsa".
Taron wasu magoya bayan kungiyar FLN AFP /FAROUK BATICHEEmmanuel Macron ya amince da hukuncin kisa kan daya daga cikin jagororin FLN shida da suka kaddamar da tawaye a ranar 1 ga Nuwamba, 1954, a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakanin Faransa da Aljeriya, musamman bayan wata muhimmiyar ziyarar aiki a Morocco.
Sanarwar ta kara da cewa, "Yin amincewa da wannan kisan gilla ya tabbatar da cewa aikin gaskiya na tarihi, wanda shugaban kasar ya fara tare da Shugaba Abdelmadjid Tebboune, zai ci gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI