Yajin aikin da ƙungiyar ma’aikatan suka tsunduma a tsakar daren jiya, ta haifar da tsaiko a babbar tashar jiragen saman ta Jomo Kenyatta da ke Nairobi.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan Moses Ndiema, ya shaidawa mambobinsa cewa za su ci gaba da yajin aikin nasu, har sai an dakatar da shirin damka wa kamfanin India na Adani ragamar ikon kula da tasha na tsawon shekaru 30, karkashin wata yarjejeniyar ƙudi ta dala biliyan daya da miliyan 850.
Wannan tsaiko dai ya sanya anga yadda fasinjoji a motoci ke dogon layi, na samun damar shiga cikin tashar.
Hukumar da ke kula da tashoshin jiragen saman Kenya, ta ce an fara gudanar da ziga-zirga kadan-kada a tashar, duk da dai alkaluma sun nuna cewa an soke tashi da saukar jiragen sama da dama a tashar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI