Likitoci a Kenya sun fara wani gangamin adawa da rashin biyansu haƙƙoƙinsu

Likitoci a Kenya sun fara wani gangamin adawa da rashin biyansu haƙƙoƙinsu

A watan Mayu shekarar nan ne yajin aikin likitocin ya kawo ƙarshe bayan shiga tsakani wanda ya kai ga gwamnati ta alƙawarta ƙarin albashi da kuma gyatta yanayin aikinsu, sai dai ƙungiyar ta KMPDU ta ce har yanzu gwamnati ba ta cika ko ɗaya daga cikin alƙawuranta ba, haka zalika ba kyautata yanayin aikinsu ba.

Cikin wata wasiƙar neman izinin gangami da shugaban ƙungiyar ta KMPDU Davji Atellah ya aikewa babban sufeton ƴan sandan Kenya Douglas Kanja ya ce tattakin zai faro tun daga ƙarfe 8 na safiyar yau Litinin daga babban asibitin birnin Nairobi inda likitocin za su yada zango a ma’aikatar lafiya gabanin zarcewa zuwa majalisar wakilan ƙasar.

Babu dai tabbacin ko rundunar ƴan sandan ta Kenya za ta bayar da cikakkiyar kariga ga masu gangamin kamar yadda suka buƙata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)