Gwamnatin hadaka ta Libiya zata fara tilastawa diya mata saka mayahi daga bakin shekaru 9 da haihuwa.
Imad Trabelsi ya kuma bayyana wasu karin matakai da ya ce zasu taimakawa wajan karfafa kyakyawan tabi’un al’umma kasar ta Libiya.
Ba ya ga wajabtawa iyaye da diya mata daga bakin shekaru 9 saka mayahi har a makarantun boko, gwamnatin nason haramatawa matan kasar yin balaguro ba tareda muharraaman su ba.
Bugu da kari gwamnatin tace haramun ne daga yanzu a rika cudanya tsakanin mata da maza a gidajen cin abinci da kuma wuraren haduwar jama’a.
Wani bangare na matakan ya kuma shafe yanke gashi da mata kanyi sai kuma shigar tufafin da gwamnatin ta ce dole tayi daidai da koyarwa al’umma Libiya.
Tuni dai aka fara kallon matakin tamkar wanda zai takaita ‘yanci da walwala a kasar yayin da ake fargaba gwamnati ta bujuro da ‘yan sanda tabbatar da da’a a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI