Firaiministan Libiya Abdulhamid Dibeybe ya ce an yanke shawarar kasarsa ta rufe kan iyakokinta ta sama da ta kasa da Tunisiya ne saboda yanayin kare kiwon lafiya ne na dan lokaci.
A cewar rubutacciyar sanarwar da fadar shugaban kasar ta Tunusiya ta fitar, shugaban kasar Tunusiya Kays Said ya tattauna da Dibeybe ta wayar tarho.
A yayin ganawar, an tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, yanayin kiwon lafiya a Tunisiya da kuma rufe iyakokin.
Dibeybe ya bayyana cewa Ministocin Kiwon Lafiya na kasashen biyu suna kan aiki tare game da rufe iyakokin.
"Libiya ta yanke shawarar rufe kan iyakokinta da Tunisiya ne saboda yanayin kiwon lafiya kuma lamarin na dan lokaci ne"
Said ya kuma bayyana cewa matsayin na gwamnatin Libiya "yan uwantaka ne" kuma ya nuna zurfin alakar da ke akwai tsakanin kasashen biyu da al'ummominsu.
Jiya, Libya ta yanke shawarar rufe kan iyakokin ta ta sama da ta kasa da makwabciyar ta Tunisiya, wacce ta ga karuwar sabbin nau'ikan cutar coronavirus (Kovid-19) a cikin mako guda daya gabata.