Firaministan Libiya, Abdulhamid Dbeibah ya bayyana cewar kasarsa ta samu kyakkyawan rabo daga iskar gas a Gabashin tekun Bahar Rum sakamakon yarjejeniyar da ta kulla da Turkiyya.
An gudanar da taron kada kuri'a a birnin Sirte don ba da kwarin gwiwa ga gwamnatin Abdulhamid Dbeibah, wanda aka zaba a matsayin Firaministan Libiya a taron da Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta jagoranta game da tattaunawar siyasar Libiya.
Abdulhamid Dbeibah wanda aka zaba a matsayin Firaminista da ya ke bayyana wa Majalisar Wakilai shirin gwamnatinsa ya ce yarjejeniyar teku da Turkiyya da Libiya suka sanya wa hannu kan hadin gwiwar tsaro da iyakar teku a shekarar 2019 tana da amfani ga kasar.
Dbeibah ya ce "Yarjejeniyar Libiya da Turkiyya a yankin Gabashin tekun Bahar Rum tana da amfani ne ga kasar ta Libiya.”
Ya kuma kara da cewa “Libiya ta samu wani kaso mai tsoka na 'yancinta na mallakar iskar gas bayan yarjejeniyar.”