Libiya ta ce a shirye ta ke ta gwabza yaki da Masar

Libiya ta ce a shirye ta ke ta gwabza yaki da Masar

Ministan Harkokin Cikin Gida na Libiya Fathi Basaga ya bayyana cewar ba sa son wani abu na cutarwa ya samu kasar Masar, amma kuma a shirye suke da su gwabza yaki da ita don kare kasarsu.

Bayan barazanar amfani da soji a Libiya da Shugaban Kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi ya yi, sai Ministan Harkokin Cikin Gida na Libiya Fathi Basaga ya fitar da nasa sakon ta shafin Twitter inda ya ce "Shugabannin 'yar uwarmu Masar sun manta da cewar al'ummar Libiya da na Masar na da tarihi, kaddara da al'adu iri daya."

Basaga ya ce "Al'ummar Libiya ba za su yarda da duk wani abu da zai cutar da zaman lafiyar Masar ba, saboda dukkan kasashen 2 za su cutu da hakan. Da jinin jama'ar Libiya aka rubuta jan layi. Jama'ar Libiya za su zauna lafiya da wadanda suke son haka. Za su iya shiga yaki ba don kai hari ba, sai don kare kasarsu.

A gefe guda Firaministan Libiya Fayyaz Sarraj ya gana da kwamandan kai Farmakan Sirte-Jufra Janaral Ibrahim Ahmad Baytulmal inda suka tattauna kan yadda za a kare fararen hula a yayin kai farmakan.


News Source:   www.trt.net.tr