Firaministan Libiya Abdulhamid Al-Dibeybe a yayin ziyarar aiki da ya kai Morokko ya gana da Shugaban Majalisar Wakilai Habib Al-Maliki a Rabat Babban Birnin Kasar.
Labaran da jaridun Morokko suka fitar sun bayyana cewa, a yayin ganawar Al-Dibeybe ya yi kira ga Morokko da ta goyawa Libiya baya a zabukan da ta ke shirin gudanarwa.
A labaran an sanar da cewa, Al-Dibeybe ya bukaci mahukuntan Morokko da su baiwa kasar cikakken goyon baya a zabukan da aka shirya gudanarwa a watan Disamban bana.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Wakilai ta Morokko Habib Al-Maliki ya bayyana cewa, ba daga waje za a warware rikicin Libiya ba, 'yan kasar da kansu ne za su warware matsalarsu a cikin gida. Kuma a koyaushe suna goyon bayan tattaunawar sulhu a tsakanin 'yan kasar Libiya.
Al-Maliki ya kuma tabo batun zabe a Libiya inda ya ce, kafa gwamnatin sulhun kasa ne mubudin farko na warware rikicin siyasar kasar.