
Tun farko hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da karuwar ‘yan gudun hijirar Sudan a Sudan ta Kudu a ƴan makonnin nan.
Kungiyar likitoci ta MSF ta ce sama da mutane 5,000 ne ke tsallaka kan iyakar kasashen biyu a kowace rana tun farkon watan Disamba sakamakon tsanantar rikici tsakanin dakarun RSF da sojojin gwamnati.
MSF ta ce sansanonin ƴan gudun hijira biyu da aka tanada sun cika maƙil, abin da ya kara kaifin bazuwar annobar kwalara da ta ɓarke a watan Oktoba cikin sauri.
MSF ta ce sansanoni biyu na Renk a Sudan ta Kudu, da aka tsara zai iya ɗaukar ƴan gudun hijira 8000 a halin yanzu suna dauke da mutane sama da 17,000.
UNHCR ta ce sama da mutane dubu 80 suka tsallaka kan iyakar ƙasashen biyu cikin ƙasa da makonni uku, galibi mata da kananan yara.
Hakan ya biyo bayan tsanantar fada a Sudan a jihohin White Nile, Sennar da Blue Nile, in ji kungiyar ta Majalisar Dinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI