Kwamandan Rundunar Sojin Ruwan Turkiyya Admiral Adnan Ozbal na ziyara a kasar Libiya.
A yayin ziyarar ta Admiral Adnan Ozbal a Libiya, ya gana da Shugaban Rundunar Sojin Kasar Muhammad Al-Sharif.
Ozbal ya tafi Libiya a ranar Litinin din nan bayan umarnin da Ministan Tsaro Hulusi Akar ya ba shi. Ya samu tarba a Tarabulus daga mahukuntan Libiya da na Turkiyya.
Admiral Ozbal ya gana da Shugaban Rundunar Sojin Libiya Al-Sharif a Sansanin Sojin Ruwa na Bu Sitte.
Kwamandan na Libiy ya bayyana gamsuwarsa game da ziyarar da Ozbal ya kai musu, kuma sun gana da juna a sirrance.